Wani Tsohon sanata daga jihar Kano ya mutu a Abuja

Legit Hausa
Allah ya yiwa tsohon sanatan Najeriya daga jihar Kano, Isa Yahaya Zarewa, rasuwa a daren ranar Litinin a Abuja.
Tsohon Sanatan ya rasu ne da misalin karfe 2:15 na daren ranar Litinin dare a gidansa dake Babban birnin tarayya, Abuja.
Majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewa sanata Zarewa ya fara jin alamun rashin lafiya yayin da yake sauraron wa'azi a wani Masallaci da ke Abuja.
A cewar majiyar, tsohon Sanatan ya kira direbansa tare da umartarsa a kan ya kai shi ofishinsa daga Masallacin, kafin daga bisani ya umarce shi ya kai shi asibiti daga ofishin nasa.
Duk da ba bayyana lokacin da za a yi masa sallar Jana'iza ba a cikin sanarwar da Legit.ng ta samu, sanarwar ta bayyana cewa jirgin sama zai dauki gawar Sanata zarewa zuwa gidansa da ke unguwar Yahaya Gusau a cikin birnin Kano, inda za a yi masa sutura.
Majiyar mu ta tabbatar da cewa ta samu labarin mutuwar tsohon Sanatan ne daga Babban hadiminsa a kafar sada zumunta (Social media) Musa Shehu Musa.
An haifi tsohon Sanata Isa Zarewa a garin Zarewa da ke karkashin karamar hukumar Rogo ta jihar Kano a shekarar 1958, kuma ya wakilci jihar Kano ta kudu a majalisar dattijai daga shekarar 1999 zuwa 2003 a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
Sanata Zarewa ya yi gwagwarmayar siyasa a jam'iyyu da dama da suka hada da SDP, PDP, APC da jam'iyyar PRP, wacce ya koma bayan ya rasa tikitin takarar Sanata a jam'iyyar APC a zaben fidda 'yan takara a shekarar 2018.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post