Wani dansanda ya yaudari abokan aikinsa bayan ya karbi cin hanci N15000

Wani faifen bidiyo da ke yawatawa a yanar gizo ya nuna yadda wani dansanda ya yaudari yanuwansa yansanda bayan ya karbi cin hancin N15.000 daga hannun wani mai mota, amma ya ce N5000 ne ya karba, bayan ya yi jayayya da matuki motar cewa sai ya bashi N20.000 amma daga bisani ya karbi N15.000.

Duk da yake bidiyon bai nuna rana ko wajen da lamarin ya farub ba, amma an ga dansandan cikin damara kuma lamari ne da jama'ar Najeriya ke kuka a kansa, inda  wasu talakawa ke zargin yansanda da tursasa wa talakawa domin karbar na goro duk da karin albashi da shugaba Buhari ya yi wa yansanda.DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post