Wa'iyazu billahi: Wata mata ta kashe yayanta 3 da jaririnta bayan ta daba masu wuka

Wata mata ta kashe yayanta guda uku bayan ta caka masu wuka sakamakon haka suka mutu a garin Awo Idemili a jihar Imo.

Kishiyar mahaifiyar matar ta ce, matar ta bukaci mijinta Emeka Ajoihe, ya je Mujami'a domin ya yi addu'a da ake kira Vigil. Ta kara da cewa bayan Emeka ya tafi ne, sai ta rufe kofa.

Daga bisani ta caka wa jaririnta mai wata 6 a Duniya wuka, ta kuma caka wa diyarta mai shekara 2, da wata diyarta mai shekara 3 wuka.

Kafin mijinta ya dawo da misalin karfe 12 na dare, jaririn tare da diyarta na biyu sun mutu, daga bisani diyarta na uku ta mutu a Asibiti.

Babu wani karin bayani dangane da wannan lamari kawo yanzu.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post