Tsananin barin wuta ya sa yan boko haram 16 sun mika wuya saura sun halaka

Ru ndunar sojin Najeriya ta bayar da sanarwar kama yan kungiyar Boko Haram guda 16 da ISWAP.

Babban jami'i mai kula da harkar yada labarai na rundunar fagen daga Col. Aminu Illiyasu ne ya shaida haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a 8 ga watan Nuwamba.

Ya ce an yi wannan nassarar ne bayan yan kungiyar sun mika wuya sakamakon fin karfinsu da soji suka yi, kuma haka ya yi sanadin mutuwar yan kungiyar da dama tare da cafke masu basu taimako  da masu basu labaran sirri.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post