Tashin hankali: Saurayi ya kashe dan uwanshi na jini saboda ya zagi budurwarshi

Legit Hausa
Jaridar Information Nigeria ta gano cewa, wannan al'amarin ya faru ne a babban birnin nan da ya zama cibiya ta kasuwanci wato garin Onitsha dake jihar Anambra.
Kamar yadda wata hirar kafar sada zumunta ta WhatsApp ta nuna, budurwar mai suna Uzor ta kaiwa saurayin nata karar kaninsa mai suna Emeka akan baya ganin mutuncinta kuma yana zaginta.
Fushin hakan ne kuwa yasa Uzor ya kudiri niyyar ladaftar da kaninsa, a sakamakon hakanne kuwa Emeka ya rasa ransa.
Karar da budurwar ta kai ita ce sanadiyyar haddasa fada tsakanin 'yan uwan.
A yayin da suke fadan ne Uzor ya dauki wuka ya bi kanin nasa da ita har yayi nasarar soka masa.
Ga dai abinda jaridar ta rubuta a kasa:
"Budurwar Uzor ta kai masa korafin kaninsa mai suna Nnaemeka cewa ya zageta kuma ba ya ganin mutuncinta, duk kuwa da cewa da Uzor da Nnaemeka basa zama inuwa daya."
"Wannan korafi da budurwar ta kai wa Uzor yasa ya fusata, hakan yasa fada ya sarke tsakanin 'yan uwan, Uzor ya dauko wuka ya bi Emeka da ikirarin sai ya kashe shi, hakan kuwa lamarin ya faru, saboda ya halakashi har lahira
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post