Ni na kashe dana mai shekara 3 domin in koya wa mijina hankali - Inji matar aure

Wata mata mai suna Rukayyat Abdulrahman ta yi ikirarin cewa ita ce ta kashe danta mai shekara 3 da kanta, domin ta koya wa mijinta mai suna Raheem hankali kwanaki kadan kafin mutuwar aurensu.
Mujallar ISYAKU.COM ya samo cewa Ganiyu  mai shekara 3, shi kadai ne Allah ya ba wadannan ma'aurata.

Rahotanni sun tabbatar cewa babu zaman lafiya tsakanin ma'auratan, sakamakon haka wata Kotun Shari'a a jihar ta ba ma'auratan kwana 90 domin su daidaita kansu, ko kuwa Kotu ta kashe aure.
Amma fa ranar Asabar 17 ga watan Nuwaamba, mazauna unguwar Olorunosebi da ke Kola Balogun na Osogbo a jihar Osun, sun wayi gari cikin rudanin jin koke koken ma'auratan, wanda suka ce basu gan Ganiyu dansu mai shekara 3 ba, duk da yake sun kwanta dalki daya tare da shi a cikin dare.

Wasu daga cikin makwabtansu sun taimaka wajen neman yaron ko ina a cikin unguwa amma basu gabn shi ba.

Amma bayan wata budurwa ta yi kokarin ta debo ruwa da safe a cikin Rijiya da ke cikin tsakiyar gidan mai hawa daya, sai ta gan Ganiyu mai shekara 3 a mace cikin Rijiya, sakamakon haka ta shida wa sauran jama'a.

Wannan lamarin ya faru ne kwana 5 kafin cikan wa'adin da Kotu ta ba ma'auratan.Nan take waani makwabci ya shiga Rijiyan ya dauko gawar Ganiyu. Sai dai wani dan haya a cikin gidan ya  ce, babu yadda za a yi yaron mai shekara 3 ya iya bude marfin rijiyar ya shiga kuma daga bisani ya rufe marfin domin marfin yaana da nauyin gaske inji dan hayan.

Yansanda sun kama iyayen Ganiyu, daga bisani suka kama makwabtan ma'auratan bisa zarginsu da hannu a wajen mutuwar Ganiyu. Ana cikin bincike ne sai mahaifiyar Ganiyu watau Rukayyat, ta shaida wa yansanda cewa ita ce da kanta ta kashe danta Ganiyu domin ta koya wa mijinta Raheem hankali domin bata son ya sake ta.

Sakamakon haka yansanda suka sallami sauran makwabta da suka kama.

Mataimakin Kakakin hukumar yansanda na jihar Osun Mustapha Katayeyanjue ya tabbatar dav faruwar lamarin
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post