Naira Triliyan daya da yan majalisa suka kashe a shekara 10 bai amfani talaka ba -Buhari

Shugaba Buhari ya ce zunzurutun kudi har Naira Triliyan 1 da yan Majalisar tarayya suka kashe cikin shekara 10 wajen ayyukan raya karkaransu bai haifar da wani sakamako mai gamsuwa ba.

Buhari ya ce kididdiga da aka tattara daga yankunan karkara a fadin Najeriya, ya nuna cewa mazauna karkara basu more ayyukan da aka ce an kashe kudi wajen yinsu ba a yakunan na karkara.

Wadannan kalaman dai, shugaba Buhari ya ambato su ne yayyin da yake jawabi a wajen wani taro da aka gudanar kan "Dushewar cin hanci da rashawa tare da aikata sauran laifuka a aikin Gwamnati" a dakin taro na fadar shugaban kasa ranar Talata.

Ofishin Sakataren Gwamnatin tarayya ne Boss Mustapha, ya shirya wannan taro tare da hadin guiwa da hukumar ICPC.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post