Matashi ya zuba guba a cikin abincin biki a Katsina

Legit Hausa
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta tabbatar da kama wani matashi, Mudasiru Tanimu, mai shekaru 18, bisa zarginsa da zuba guba a cikin abin sha da aka raba a wurin wani biki a kauyen Barhim da ke yankin karamar hukumar Batagarawa a jihar.
A cikin wani jawabi mai dauke da sa hannun kakakinta (PRO), SP Gambo Isah, da ta fitar a ranar Alhamis, rundunar 'yan sandan jihar ta ce Tanimu ya hada kai da wani matashi, Nafiu Umar, mai shekaru 18 domin saka gubar a cikin abincin 'yan bikin.
"Rundunar 'yan sanda ta kama Tanimu, wanda ke zaune a kauyen Barhim.
"Ya samu taimakon wani matashi mai suna Nafiu Umar wajen aikata laifin da ake tuhumarsa da shi," a cewar SP Isah.
Kakakin ya bayyana cewa yanzu haka Nafiu ya cika wandonsa da iska bayan amun labarin an kama Tanimu.
"Sun hada wata guba ne mai bugar wa da suka zuba a cikin Zoborodo da aka raba wa 'yan biki a kauyen Barhim da ke yankin karamar Batagarawa.
"Hankalin wani mutum, Iliya Musa, mai shekaru 25, da wata matashiya mai shekaru 16 ya gushe nan take bayan sun sha Zobon da matasan suka zuba gubar a ciki.
"An garzaya da su babban asibitin Katsina, inda likitoci suka tabbatar da cewa Musa ya mutu yayin da ita kuma matashiyar suka ce bata cikin hayyacinta," a cewar Kakakin rundunar 'yan sanda, SP Isah.
A cewar rundunar 'yan sandan, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma rundunar na cigaba da gudanar da bincike domin ganin ta cafke daya matashin da ya gudu.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post