Magoya bayan APC sun babbake wata jigon PDP har lahira a jihar Kogi

Rahotanni daga jihar Kogi sun tabbatar da cewa wasu yan daban siyasa magoya bayan jam'iyar APC sun kone shugaban yakin neman zabe na matan PDP Mrs Acheju Abuh har lahira a garin Ochadamu da ke karamar hukumar Ofu a jihar Kogi

Mujallae ISYAKU.COM ya samo cewa Kakain hukumar yansandan jihar Kogi, DSP Aya Williams ne ya tabbatar da haka a wata takardar sanarwa da ya fitar kan lamarin.

DSP Aya ya ce " Ranar 18/11/2019 da misalin karfe 4:30 na yamma, wani mutum mai suna Musa Etu da ke garin Ochadamu a karamar hukumar Ofu ya kawo kara a caji ofis na yansanda cewa, da misalin karfe 10:30  na wannan rana an sami rashin jituwa tsakanin wani mutum mai suna Awolu Zekeri dan shekara 35 kuma magoyi bayan jam'iyar APC, da kuma wani mutum mai suna Gowon Simeon magoyi bayan jam'iyar PDP, dukkansu yan garin Ochadamu.

Sakamakon haka Gowon Simeon ya daba wa Awolu Zakeri wuka a cinya , bisa wannan rauni Awolu ya mutu a kan hanyarsu ta zuwa Asibiti.

Sakamakon haka fusatattun matasa suka dunguma zuwa gidan wani mutum mai suna Simorn Abuh da ke garin, wanda kawun Gowon ne, daga bisani matasan suka banka waa gidansa wutu, kuma wannan mataki ya yi sanadin babbakewar wata tsohuwa mai suna Salome Abuh  mai shekara 60 a Duniya. Hakazalika an kone wasu gidaje guda uku.

An adana gawar a dakin ajiye gawa na Asibitin koyarwa na Jami'ar Anyigba domin gudanar da binciken gawa. An tura jami'an rundunar yansandan kwantar da tarzoma domin tabbatar da tsaro".
  
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post