Labarin wani Sarki mai hikima da yan majalisarsa


A zamanin da ,a Birnin Fahshar an yi wani Sarki mai suna Sultamari wadda mulkinsa cike yake da adalci da son daidaita gaskiya a tsakanin al'umma.

Wata rana sai manyan mutane a garin kamar su Wazirin,Ubandawaki,Shamaki,Shantali da dai sauransu suka je gurin Sarki Sultamari a yayinda yake a cikin gonar Lambun sa inda yake hutawa sai suka fadi suka yi gaisuwa.

Sarki ya amsa gaisuwarsu sai yace da Waziri, yau lafiya kuwa aka biyo ni har cikin Lambu? Waziri yace Lafiya kalau ran Sarki ya dade face mun zo ne da wata bukata guda daya amadadin jama'ar gari.

Sarki yace to miye wannan bukatar? Waziri ya shaida masa cewa sun kula cewa Karuwai sun yi yawa a garin kuma hakan zai iya bata masu yara da tarbiyyar su.

Sai Sarki yace ku dakata ina zuwa,sai ya tashi ya dauki buta ya  je ya kama ruwa sai ya dawo ya zauna ya cire hula yayi alwala sai ya dauko Alkur'ani ya daga yayi rantsuwa da Allah cewa shi bai taba ZINA ba, kuma yana son kowane mutum a cikinsu ya tashi yayi Alwala yayi rantsuwa akan cewa bai taba yin zina ba tunda Mahaifiyarshi ta haife shi.

Gabadaya dai babu wadda ya iya yin abin da Sarki ya yi....sai Sarki yace ku tashi ku tafi ku tarbiyantar da kanku da 'ya'yanku

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN