Labari cikin hotuna: Maciji mai tsawon kafa 8 ya shake wata mata har lahira

Yansanda sun sami  gawar wata mata mai suna Laura Hurst mai shekara 36 bayan wani maciji mesa  mai tsawon kafa 8 ya laulaye wuyanta ya shaketa ta mutu a Battle Ground da ke Indiana a daren Laraba.

Mujallar isyaku.com ya samo cewa akwai macizai guda 140 kala kala a cikin wannan gida da Don Munson waanda Sheriff na yankin Benton ya samar domin kiwon macizai.

Sai dai wata sanarwa da ta fito daga Sajent Kim Riley na yansandan Indiana, ya ce Hurst ta ajiye macizai 20 wanda take kiwo , kuma tana ziyartar gidan sau biyu a mako.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post