Labari cikin hoto: Wata al'umma ta kori wani dan iska daga garinsu har abada

An kori wani kusurgumin dan iska da ya addabi al'umman Agudama Epie a Yenagoa babban birnin jihar Baayelsa daga garin har abada.


Ana zargin wannan cikakken dan iska wanda aka fi sani da suna "Supreme" da aikata fashi, fyade da kasancewa dan kungiyar asiri.

An sami nasarar koran Supreme kwata kwata daga garinsu bayan ya sha dan karen duka, a hannun matasan kungiyar AYM, karkashin jagorancin shugan kungiyar Comr Prudent Ezibeyame.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post