Kwastoma ya tube wandonsa bayan ma'aikaciyar wutan lantarki ta yanke masa wuta - Bidiyo

Wani fusataccen mutum ya tube wandonsa sakamakon haka ya bayyana tsiraicinsa a bainar jama'a yayin da yake jayayya da wata ma'aikaciyar wutan lantarki PHCN bayan ta yanke masa wuta, kuma ta yi kokarin tafiya da wayar da ta yanke a birnin Ikko, watau Lagos.

Sakamakon cire wandonsa da ya yi, ala tilas ma'aikaciyar wutan lantarki ta saki waya ta gudu nan take.

Kalli bidiyon yadda lamarin ya faru:DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post