Ko jam'iyar APC za ta dusashe bayan Buhari a 2023 ?

Yayin da farin jini da tsarin gaskiyar shugaba Muhammadu Buhari ya zama daya daga cikin babban madogara da jam'iyar APC ta amfana da shi wajen cin zabukan da aka gudanar a Najeriya daga 2015 zuwa yau, sai ga lamari ya fara canjawa sakamakon wasu manyan kura kurai da yayan jam'iyar APC suka tafka a duk matakai na siyasa daga kananan hukumomi, jihohi da kuma tarayya.

A mataki na atarayya, shugaban jam'iyar APC Adams Oshiomhole, ya ketare rijiya da baya, bayan ya tsallake kuri'ar kin  mincewa da shi a matsayin shugaban jam'iyar, wanda ya samo asaali daga zarge-zarge da aka yi masa kan lamurra da suka shafi salon shugabancin jam'iar.

A jihar Kebbi, yayan jam'iyan ne suka yi ta korafi mai zafi, dangane da abin da suka kira rashin adalci a lokuttan zabukan kananan hukumomi da hukumar zabe ta jihar ta gudanar. Jama'a da dama sun yi ta korafi da zargin cewa  an yi masu dauki dora ne amma ba zabe ba.

Sai dai hukumar zabe na jihar Kebbi tana kan bakanta na cewa ta gudanar da zaben kananan hukumomi kamar yadda doka ta tanada.

Sakamakon rudani da ake zaton ya bayyana a cikin jam'iyar APC a mataki na jihohi kamar jihar Kebbi, inda yan jam'iyar suka dinga fitowa a kafafen watsa labarai suna kalubalantar jam'iyar, kafin da kuma bayan zaben 2019, da matakin tarayya  inda shugaban jam'iyar Adams Oshiomhole ya sha kahon zuka daga yayan jam'iyar. Za a iya cewa APC ta fara rasa martabarta a tsakanin yayanta da talakawan Najeriya kenan ?.

SHARHI

Sakamakon yadda lamurra ke ta tabarbarewa a cikin jam'iyar APC a  matakai na kananan hukumomi da tarayya, ganin yadda yayan jam'iyar ke nuna wa juna yatsa a duk matakai. Haka zalika bincike ya nuna cewa rinjayen yan jam'iyar APC tun asali yan jam'iyar PDP ne, kuma sun more shugabanci ko  mukamai sakamakon kasancewac a cikin jam'iyar PDP kafin su canja sheka zuwa jam'iyar APC a zabukan 2015.

Yawancin wadanda suka baro jam'iyar PDP suka koma APC sun kasa samun madogara ne a cikin PDP bisa buri da suka sa a gaba a wancan lokaci, da basu samu ba  , sai suka tsallake zuwa APC wanda haka ke nuna cewa ba wai sun shiga APC domin akidar Buhari ne ba ko APC, amma sai dai domin neman biyan bukatan kansu na samun kujerun mulki, kuma sun samu domin albarkacin daraja, dattaku, mutunci, rikon amana, tare da kishin kasa irin na shugaba Buhari.

Wannan yana nuna cewa, bayan shugabancin Buhari a 2023, ba mamaki watakila jam'iyar APC za ta zo karshe idan ba tare da Buhari ba.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post