Kano ne birni mafi gurbacewar iska a Afirka - Rahoto


BBC Hausa
Rahoton dai ya ce birnin Kano ne ke da mafi gurbacewar iska a fadin nahiyar Afirka, inda gurbacewar iskar ta kai kashi 53.4 cikin dari.
Dangane da dalilan da suka haddasa gurbacewar iskar, rahoton ya zayyano wasu abubuwa kamar haka;
  • Amfani da itace da kananziri da gawayi yayin girki
  • Dagwalo da sharar gona
  • Hayakin ababan hawa
Rahoton ya kuma nuna cewa birnin Kampala ne ke biye wa na Kano a gurbacewar iskar, inda birnin Fatakwal na Najeriya ya zama na uku sannan birnin Adis Ababa ya zamo na hudu a jadawalin gurbatacciyar iskar.
KnaoHakkin mallakar hotoWORLD AIR QUALITY REPORT
Image captionKano da Kampala da Fatakwal da Adis Ababa
Har wa yau, Da farko dai rahoton wanda cibiyar IQ Airvisual mai sansani a kasar Switzerland ta fitar, ya sanya Najeriya a matsayin kasa ta 10 mafi gurbacewar yanayi a duniya.
Rahoton ya ce gurbatacciyar iska da ke Najeriya ta kai kashi 44.8 cikin 100, inda Uganda da Ethiopia suke biye mata baya.
NajeriyaHakkin mallakar hotoWORLD AIR QUALITY REPORT
Rahoton na cibiyar IQ Airvisual ya ce nahiyar Afirka na fama da gagarumin rashin hanyar tattara bayanan bibiyar iska mai inganci, yayin da kuma take fuskantar kalubalan gurbacewar iska masu alaka da ita kanta nahiyar.
Ya ce Afirka na da bunkasar birane mafi sauri ga kuma karuwar jama'a da ke kwarara zuwa manyan birane, inda gurbatacciyar iska ta fi yawa.
Kuma manyan kafofin gurbatacciyar iska sun hadar da amfani da makamashi irinsu gawayi da itace da kananzir wajen girki, lamarin da ya sa matsalar ta zama gagara badau a yankunan karkara saboda takaitattun kayan more rayuwa da hanyoyin samun makamashi mai tsafta.
KanoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionBirnin Kano na da cinkosan jama'a da na ababan hawa
KanoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionKano na da yawan masu Adaidaita sahu
Masana sun ce gurbatacciyar iska ce sanadi na hudu a duniya mafi tasiri wajen haddasa mutuwar fu-ju'a.
Rahoton ya ce kasar Bangaladesh ce ta fi rashin iska mai inganci a tsakanin kasashen duniya, inda take da gurbatacciyar iska kashi 97.1 ,sai k'asar Pakistan, Indiya kuma na biye musu da gurbatacciyar iska kashi 72.5.
Rahoton ya ce Najeriya, ita ce k'asa ta goma a duniya kuma mafi gurbatar yanayi a fadin nahiyar Afirka, inda take da gurbatacciyar iska har kashi 44.8 cikin 100. Sai Uganda a matsayi na biyu, Ethiopia, matsayi na uku.
Binciken na cibiyar IQ Airvisual ya ce gurbatacciyar iska, gagarumar kasadar muhalli ce ga lafiyar mutane a yau, inda kiyasi ya ce matsalar na janyo mutuwar bakwaini miliyan 7 duk shekara a duniya.
KanoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMasu dibar kasa a jakai a cikin birnin Kano na taimaka wa wajen gine-gine irin na gargajiya
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post