Jami'ar sufuri: Buhari ya dira Katsina ya zarce zuwa Daura a jirgi mai saukar Angulu

Isyaku Garba Zuru

Shugaba Buhari ya dira birnin katsina tare da tawagarsa ta manyan jami'an gwamnati. Shugaban yana kan hanyarsa ce ta zuwa Daura.

Buhari ya isa Katsina da misalin karfe 4:42 na yamma, inda Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari tare da Matainakinsa Mannir Yakubu, da wasu yan majalisar zartarwa na jihar Katsina suka tarbi shugaba Buhari tare da tawagarsa.

 Daga bisani Buhari ya zarce zuwa Daura da misalin karfe 5:04 na yamma a jirgi mai saukar Angulu. Ana kyautata zaton Buhari zai halarci taron assasa Jami'ar sufuri a Daura daga cikin jerin ababe da zai yi.

President Buhari, thereafter, headed to Daura at about 5:04 pm aboard a helicopter.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post