Inna Lillahi: Wata mata ta kashe jariri da ta haifa a birnin Kano

Legit Hausa

Ba hoton jaririn bane
Freedom Radio ta wallafa rahoton cewa jami'a sintiri a unguwar Kawo da
ke cikin birnin Kano sunsamu nasarar cafke wata mata mai suna Aisha
Muhammad bisa zarginta da hallaka jaririn da ta haifa a cikinta.

Am cewar rahoton, wata matashiya ce ta fara tona asirin Aisha yayin da ta
iske gawar jaririn bayan ta shiga gidan da matar ta haihu, ita kuma ta
kwarmata labarin har ta kai ga jami'an sintirin unguwar sun shigo
cikin lamarin.

Amma a nata bangaren, Aisha ta bayyana wa wakilin gidan
Radiyon Freedom, Aminu Abdu Baka Noma, cewa bata kashe jaririn ba duk
da kasancewar ta haife shi ne ba tare da aure ba, kawai karar kwana ce
da kaddara suka yi sanadin mutuwarsa.

Mahaifiyar Aisha ta shaida wa Freedom Radio cewa diyarta bata kashe jaririn da ta haifa ba, amma
tana rokon a kashe maganar a wurin, saboda, a cewarta, wani
makwabcinsu ne ya ci amanarsu ya dirka wa diyarasu ciki.

Mallam Shehu Adamu, sakataren 'yan sintiri na yankin Kawo ta Arewa, ya bayyana cewa
basu bata lokaci ba wajen zuwa gidan su Aisha bayan samun labarin
abinda ake faruwa, inda suka taho da yarinyar da mahaifiyarta da kuma
gawar jaririn da ake zargin kashe shi Aisha ta yi. Sakataren ya kara
da cewa zasu mika Aisha da Mahaifiyarta ga jami'an tsaro domin su
zurfafa bincike a kansu.
Previous Post Next Post