Ina yar shekara 16 na auri mijina, ko firamari ban yi ba - Uwargidar gwamnan Bauchi

Legit Hausa

Aishatu Mohammed, Uwargidar gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ta
bayyana a ranar Asabar cewa bata yi karatu ba lokacin da ta auri
mijinta. Haijya Aishatu ta bayyana hakan ne a jihar Bauchi a taron da
kwamitin tallafin kananan yaran ta majalisar dinkin dunya UNICEF.
Tace:

"Ina yar shekara 16 kuma a jahilce lokacin da na auri mijina."
"Mu yara mata 100 ne a danginmu; babu wacce tayi karatun Boko cikinmu;
sai da na haifi yara uku na fara karatu."

 "Dalilin haka shine iyayenmu basu yarda da ilmantar da diya mace ba; na yi kokarin zuwa makaranta
amma basu yarda ba."

"Na kudirci zuwa makaranta daga yayyuna bayan haihuwana na uku, na nace sai da mijina ya samar mun malami a gida."

"Da haka na fara sannan na tafi makarantar sakandare. Yau na kammala
karatun Digiri a jami'ar Abuja."

Ta bayyana yadda rashin ilmantar da yara mata da aurar da su da wuri yayi tsamari a jihar inda ta daura laifin kan iyaye da sukayi imanin cewa diya mace ba ta bukatar zuwa
makaranta.

Hajiya Aisha ta jaddada muhimmancin ilmantar diya mace da
kananan yara ga baki daya saboda hakan zai rage yawan laifuka rashin
tarbiyya cikin al'umma.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN