Hotuna: Buhari ya karrama hafsan kwastam da ya ki karbar cin hancin N150 miliyan

Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama wasu ma'aikata guda biyu da suka hada da Bashir Abubakar na hukumar hana fasa kwabri na kasa watau NCS da Mrs Josephine Ugwu na ma'aikatar Filayen jiragen sama na Najeriya saboda nuna mutunci da amana a yadda suke gudanar da ayyukansu.

Mataimakin Kontorola na hukumar hana fasa kwabri Abubakar Bashir, ya ki karbar cin hanci na zunzurutun kudi har Dala 412.000 daidai da Naira Miliyan dari da hamsin a kudin Najeriya (N150 Million) domin a shigo da Kwantena 40 makare da Kwayar Tramadol mai sa maye, amma ya ki ya aminta da haka.

Ita kuma Mrs Ugwu wacce mai aikin shara ce a ma'aikatan jiragen sama na Najeriya, ta sha mayar da kudi da take tsinta ga masu kudin yayin gudanar da aikinta na shara, daga ciki har da Dala Miliyan goma sha biyu( 12 million Dollars) da wani ya manta a cikin ban daki na filin saukan jirage da take aiki ta tsinci kudin kuma ta mayar da su ga maishi.

Buhari ya gabatar da lambar yabon ne ga mutanen a wajen bude wani taro na kwana biyu kan " Dusashewar cin hanci da rashawa da wasu laifuka a ayyukan Gwamnati" wanda ake gudanarwa a dakin taro na Fadar shugaban kasa.

Ofishin Sakataren Gwamnatin tarayya ne ke gudanar da taron tare da hadin guiwa da hukumar ICPC.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post