Gwamnan Zamfara ya rattafa hannu a kan dokar haramta biyan tsofaffin gwamnoni kudin fansho

Legit Hausa

Gwamnan jahar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya rattafa hannu kan kudurin haramta biyan tsofaffin gwamnonin jahar kudaden fansho inda suka lakume miliyoyi, da wannan sa hannu na gwamna kudurin ta zama doka.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Gwamnan ya rattafa hannu a kan kudurin dokar ne a ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba a ofishinsa dake fadar gwamnatin jahar Zamfara, daga cikin wadanda suka halarci taron rattafa hannun akwai kaakakin majalisar dokokin jahar da dai sauransu.
Idan za’a tuna, a ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba ne gwamnatin jahar Zamfara ta soke dokar da ta tilasta ma gwamnatin jahar Zamfara biyan tsofaffin gwamnoni miliyoyin kudade a matsayin kudin fansho, tare da haramta biyan gaba daya.
Wadanda suke amfana da wannan doka sun hada da tsofaffin gwamnoni, tsofaffin mataimakan gwamnoni, tsofaffin kaakakin majalisa, tsofaffin mataimakan kaakakin majalisa, inda gwamnati ke biyansu makudan miliyoyi a duk wata da kuma sauran alfarma daban daban.
Majalisa ta soke wannan doka ne bayan bayyanar wata wasika da tsohon gwamnan jahar Abdulaziz Yari ya aika ma gwamnatin jahar Zamfara yana neman ta biyashi hakkinsa na fansho, wanda ya kai naira miliyan 10 a duk wata, kamar yadda yace dokace ta tanadi haka, kuma a ranar 23 ga watan Maris na 2019 aka yi dokar.
Faruk Musa Dosara daga mazabar PDP Maradun 1 ya fara gabatar da kudurin dokar, inda ya majalisar ta duba kudurin a matakin gaggawa domin kawar da dokar dake bukatar biyan tsofaffin shuwagabannin siyasa makudan kudade.
A cewar dan majalisan, tsofaffin shuwagabannin siyasan suna lakume kimanin naira miliyan 700 a duk shekara, daga nan sai dan majalisa Tukur Jekada Birnin Kudu ya goyi bayan kudurin dokar.
Daga karshe bayan tafka doguwar muhawara zazzafa, kaakakin majalisar, Nasiru Mu’azu Magarya ya sanar da amincewa da kudurin dokar, sa’annan ya bukaci a mika ma gwamnan jahar domin ya rattafa hannu a kanta.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post