Dansanda ya bindige mutum har lahira inda wani Gwamna ke halartar daurin aure

Wani dansanda ya bindige wani mutum yayin wani bikin aure da Gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel ya halarta'

Dansandan ya bindige mutumin ne ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba a Ikot Ukab da ke karamar hukumar Nsit Ubium a jihar Akwa Ibom.

Rahotanni sun ce wanda aka kashe sunansa Godwin Thomas, amma an kasa gane dansandan da ya harbi Godwin kuma ya kashe shi har lahira yayin da Gwamna Emmanuel yake zaune tare da dimbin mutane a wajen bikin auren.

Sanarwar yansanda ta ce jama'a sun halarci wajen daurin auren kuma yanayi abin sha'awa, amma akwai wasu yansanda da suka zo tare da wasu manyan mutane daga ciki da wajen jihar Akwa Ibom domin tsaron rafiyar manyan mutane da suke tare da su.

Amma Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta hannun Kwamishinan watsa labarai ya ce, Gwamna Emmanuel bai ji dadin wabbab lamari ba, ya kuma bayar da umarnin cewa wajibi ne a gano tare da hukunta wanda ya aikata wannan kisan wanda bai ji bai gani ba.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post