Dansanda ya bindige kansa har lahira sakamakon rashin karin mukami

Isyaku Garba Zuru

Wani jami'in dansanda mai suna Sgt Paul Joseph wanda aka tura aiki a bankin Access da ke mahadar Ahiara a Ahiazu da ke karamar hukumar Mbaise a jihar Imo, ya dauki ransa da kansa bayan ya bindige kansa har lahira sakamakon rashin karin mukami.

Wata majiya ta ce, Paul ya dade a kan mukamin Saje (Sergeant) kuma ya fito ne daga jihar Taraba, ya cancanta a kara masa girma zuwa Safeto ( Inspector) amma haka bai samu ba.

Da karfe 7 na safe ranar Laraba, Paul ya shiga dakin tsaro da ke kofar shiga Bankin, daga bisani aka ji karar tashin bindiga. Bayan ma'aikatan Bankin sun ruga zuwa dakin ne sai suka tarar da abin da ya faru.

Kakakin hukumar yansanda na jihar Orlando Ikeokwu ya tabbatar da faruwar lamarin  ya ce an kai gawar dansandan dakin ajiye gawa.

Kwamishinan yansandan jihar Rabiu Ladodo ya bayar da umurnin cewa a gudanar da bincike kan lamarin.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post