Chiyamomin kananan hukumomi 7 da kansiloli 42 sun canja sheka daga PDP zuwa APC a Ekiti

Shugabannin kananan hukumomi guda bakwai tare da Kansiloli arba'in da biyu wanda ke kan kujerar mulki, sun canja sheka daga jam'iyar PDP zuwa jam'iyar APC da ke mulki a jihar Ekiti.

Wannan ya biyo bayan wani taro ne da aka yi a dandalin Fajuyi inda shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Biodun Omoloye ya karbe su amadadin Gwamna Kayode Fayemi.

Wadanda suka canja shekan , sun yi alkawarin za su yi aiki tukuru domin fuskantar zabe da za a yi na kananan hukumomi a jihar ranar 7 ga watan Disamba.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post