Buhari zai bude iyakokin Najeriya a shekarar 2020, karanta dalili

Legit Hausa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da kara tsayin wa'adin
atisayen da aka yi wa lakabi da 'Exercise Swift Response' wanda ya
jawo aka rufe iyakokin Najeriya na kasa da makwabatan kasashe. An rufe
iyakokin Najeriya ne tun ranar 20 ga watan Agusta, kuma ana saka ran
bude iyakokin a ranar 31 ga watan Janairu, sabanin tsammanin da wasu
ke yi na cewa za a bude iyakokin kafin lokacin bikin Kirsimeti domin
'yan kasuwa a yankin kasashen Afrika ta yamma su samu su sarara.

A cikin wata sanar wa mai lamba kamar haka: NCS/ENF/ABJ/221/S.45 mai
dauke da sa hannun Victor David Dimka, shugaban sashen tilasta biyayya
ga dokokoki a hukumar Kwastam, ya ce sun samu takardar neman su yi
biyayya ga umarnin dakatar da atisayen daga ranar 31 ga watan Janairu.
An fitar da takardar sanarwar ne ranar 1 ga watan Nuwamba, 20 "An
umarce ni na sanar da ku cewa duk da an samu gagarumar nasara ta
fuskar tsaro da tattalin arziki sakamakon rufe iyakokin Najeriya na
kasa, har yanzu akwai wasu manufofi da gwamnati ke son ta cimma.

" A saboda haka ne shugaban kasa ya amince da kara tsawon wa'adin atisayen
da ake yi zuwa ranar 31 ga watan Janairu, 2020. "Ana bukatar dukkan
hukumonin tsaro da su sanar da jami'ansu, dake cikin aikin atisayen,
wannan sabon canji da aka samu. "Za a biya dukkan jami'an da ke cikin
atisayen kudinsu na alawus da zirga-zirga na tsawon wa'adin da aka
kara ba tare da wani bata lokaci ba," kamar yadda yake a cikin
sanarwar.

A ranar 20 ga watan Agusta ne shugaban hukumar kwastam,
Hameed Ali, ya sanar da fara atisayen "Exercuse Swift Response" wanda
ya kunshi dakarun soji da sauran jami'an hukumomin tsaro na ksa domin
kawo tsafta da gyara a kan iyakokin Najeriya na kasa da ake amfani da
su wajen shigo da kayan da dokar kasa bata amince da shigo wa da su.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN