Bidiyon yadda wani sojan Najeriya ya tono jariri sabuwar haihuwa da aka binne da ranshi

Legit Hausa
Wani soja a rundunar sojin Najeriya ya fitar da wani bidiyo mai cike da abun takaici da alhini. Bidiyon dai ya fantsama kafafen sada zumunta na zamani inda yake ta jawo kace nace a wajen jama'a.
A bidiyon kuwa, an nuna yadda wasu suka ceto rayuwar wani jariri wanda aka binne da ranshi a wata jiha dake nan arewacin Najeriya.
Kamar yadda shaidu suka bayyana, mahaifiyar jaririn ce ta binneshi saboda ba zata iya daukar dawainiyarshi ba. Masu wucewa ne suka dinga jin kukan jaririn, Hakan kuwa yasa suka tona ramin, bayan tona ramin mutanen sun tarar da jaririn da ranshi.
Jaririn yayi wajen awanni bakwai a rufe a cikin kasa kafin a samu damar ceto shi. An garzaya da jaririn zuwa asibiti mafi kusa inda yake karbar kulawar ma’aikatan lafiya.
Wannan na nuna babu wanda ya isa ya kauce kaddararsa, domin kuwa kaddara tsarin Ubangiji ce ba mutum ba.
A wani labari da Legit.ng ta ruwaito, an ji kauyuka 67 a babban birnin tarayya Abuja, inda ake kashe tagwaye, zabiya da kuma yaran da mahaifiyarsu ta rasu wajen haihuwa.
https://www.youtube.com/watch?v=KHPhR2riQvM
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post