Bidiyo: Yadda wasu yansanda suka yi wa dan acaba duka

Wani faifen bidiyo da ke zagayawa a yanar gizo, ya nuna yadda wasu yansanda suka dinga dukan wani da ake kyautata zaton cewa dan acaba ne, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Babu wani cikakken bayani kan inda lamarin ya faru, ko musabbabin da ya sa aka gan yansandan suna dukan dan acaban, daga bisani kuma an gan wani dansanda yana kokarin hawan babur da ake zaton na dan acaban ne.

KALLI BIDIYO:Wannan yana faruwa ne kwanaki kadan bayan an gan wani faifen bidiyo da ya nuna yadda wani jami'in dansanda ya karbi cin hancin N15.000, amma ya ce wa abokan aikinsa cewa N5.000 ya karba daga wajen wani mai mota. Lamari da ya sa mahukuntan hukumar ta yansanda suka kama tare da hukunta jami'in dansandan.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post