Bidiyo: Wani Gwamna ya kuru bayan yan daban siyasa sun mamaye shi a Otel

Wasu da ake kyautata zaton cewa yan daban siyasa ne a jihar Kogi sun kai hari ida suka mamaye Otel na Gwamnan Oyo Seyi Makinde, amma jami'an tsaro masu tsaron lafiyarsa suka shawo kansu.

An ji wani fusatacce cikin matasan da suka mamaye Otel na Gwamnan yana cewa a cikin faifen bidiyo " Wannan gallazawa ya yi yawa a wannan kasa" kuma ya yi ta maimaita wannan kalma.

Ranar 16 ga watan Nowamba ne ake shirin gudanar da zaben Gwamnan jihar Kogi.

Gwamna Seyi Makinde, masu ruwa da tsaki tare da wasu Gwamnonin PDP, sun hallara jihar Kogi domin baiwa dan takaran Gwamnan jihar Kogi a jam'iyar PDP kwarin guiwa. Engr. Musa Wada ne ya tsaya takaran kujeran Gwamna a jam'iyar PDP.

An ga wasu jami'an tsaron Gwamnan suna zaro kananan bindigogin hannu watau Pistol, yayin da yansanda suke a cikin shirin ko ta kwana,  sa'ilin da yan daban suka mamaye otel da Gwamnan yake ciki.

Kalli bidiyo a kasa:DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post