Barnata transfoma: Matasa sun kashe barayin wayan wutan lantarki 3 sun kone gawar 1

Wasu matasa daku fataken dare guda uku, sun sha dan karen duka a hannun wasu fusatattun matasa, sakamakon haka rai ya yi haklinsa yayin da aka banka wa gawar daya daga cikinsu wuta ta kone kurmus a garin Umuohiagu da ke Ngor Okpala a Egbelu Obube da ke karamar hukumar Owerri ta arewa a jihar Imo.


Wadanda aka halaka su ne Ifeanyi Mgbakabala da Kelechi Eke(aka Agwo) wadanda yan asalin Amagwa ne da ke kauyen Umuagwu a karamar hukumar Umuohiagu, yayin da aka kasa gane asalin cikon na uku daga cikinsu.

Kafin su gamu da ajalinsu, ana zargin matasan da aikata fashi da makami, sace sace, da satar wayoyin Transfoma na wutan lantarki a wannan yankin.

Bayanai sun ce kafin rana ta bace, barayin sun lalata Tranfomomi 8 a yankin, kuma sakamakon haka suka jefa yankin gaba daya cikin rashin wutan lantarki.  Amma lokacin da suke sace wayoyin wuta a transfoma guda daya tilau da ya rage, sai asirinsu ya totu, kafin matasa su aika su barzahu.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

 Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post