APC ta yi babban nasara bayan Kotu ta soke zaben wani Gwamna

Legit Hausa

Kotun daukaka kara da ke zama a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo ta
soke zaben Gwamna Seyi Makinde na jihar. A cewar jaridar Daily
Nigerian, kotun ta yanke hukunci ne a karar da Adelabu na jam'iyyar
All Progressives Congress (APC) ya daukaka.

Kotun ta dage hukuncin kotun sauraron karar zabe wacce ta jaddada nasarar Makinde. Sai dai
kuma, kotun ba ta kaddamar da Adelabu a matsayin wanda ya yi nasara
ba. Kotun ba ta kuma yi umurnin sake sabon zabe ba. A halin da ake
ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Seyi Makinde ya bayyana cewa ya
kwashe tsawon shekara 13 na rayuwarsa wajen siyar da biredi a bakin
asibitin Adeoyo a Ibadan, kafin ya zama Gwamnan jihar Oyo.

Gwamnan na jihar Oyo ya bayyana hakan ne a wajen bikin cikar mahaifiyarsa, Misis
Abigael Makinde shekara 80 wanda aka gudanar a cocin St Paul Anglican
Church da ke Yemetu a ranar Lahadi, 10 ga watan Nuwamba, cewa ya zama
wani mai fada a ji ne ta hanya samun ilimi.

A cewarsa, ya kaddamar da ilimi kyauta a jihar ne domin ganin cewa mazauna jihar sun amfana
wajen samun ingantaccen ilimi. Gwamna Makinde ya kuma bukaci iyaye a
jihar da su dauki karatun yaransu sama da komai.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN