An yi nasarar raba yatsun kafa na saurayi da aka haifa da yatsu 9 a kafarsa

Wani saurayi dan shekara 21 mai suna Ajun dan kasar Sin, watau China, wanda aka haifa da yatsun kafa guda tara, ya fuskanci tiyata inda aka yi nasarar yanke sauran yatsu da suka tsiro a tsakakanin sauran yatsu da ya yi dai dai da na bil'adama kamar yadda aka saba gani.

Dr Wu Xians wanda likita ne a Asibitin Shunde Heping Surgical Hospital a yankin Foshan, wanda shi ne ya yi nasarar yi wa Ajun tiyata na tsawon awa tara, ya ce wannan lamari ga dan shekara 21 wani abu ne da ba safai aka samu ba a cikin al'umma.

Ya ce hakan na faruwa ga mutum daya a cikin mutum 700 zuwa 1000.

Tun farko daoi, iyayen Ajun sun ki zuwa Asibiti tun da wuri domin sun yi amanna cewa wannan halitta na yatsu tara a kafar dansu Ajun, kyauta da wata daukaka ce daga Allah.
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post