An kashe direban gidan rediyo yayin da aka kai wa yan PDP farmaki a zaben Bayelsa

Rahotanni daga jihar Bayelsa sun nuna cewa wasu matasa yan jam'iyar APC sun kai wa wasu 'yan jam'iyar PDP hari yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kamfen a Nembe na jihar Bayelsa.

An kashe direban motar OB na gidan rediyon Bayelsa a wannan hari, Mr Simon Onu, ya mutu  ne bayan yan iska da ake zargin yan APC sun harbe shi da bindiga, yayin da sauran yan PDP suka nemi mafaka a cikin daji.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post