An gano gawar wata mata da aka daureta da dutse aka jefa cikin rijiya

Wasu batagari sun sace, kuma suka halaka wata mata da ke bayar da rancen kudi da ake kira AKAWO, bayan sun daureta da wani katon dutse suka jefata a cikin wani rijiya a birnin Port Harcourt.

An lura cewa an huda silin na gidanta da take zaune a ciki, inda ake kyautata cewa ta nan ne maharan suka shiga dakinta.

Wacce aka kashe mai suna Miss Charity Ohaka, ta fito daga garin Okporovo Oghakiri ne a karamar hukumar Emohua a jihar Rivers.

Wannan lamarin ya sa wasu fusatattun matasa suka bazama a unguwar, suka dinga fasa gilasan wasu motoci tare da dukan jikinsu.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post