Yanzu-yanzu: An tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi

Ana saura wata daya gudanar da zaben jihar, an tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba. Majalisar dokokin jihar sun tsige Mista Achuba ne a Lokoja, babbar birnin jihar, ranar Juma'a 18 ga Oktoba, 2019. Shugaban masu rinjaye a majalisar ya bayyana hakan ne ga manema labarai a zauren majalisar. Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Wani kwamitin binciken a kan zargin da ake yiwa mataimakin gwamnan Kogi Simon Achuba, wanda Barista John Baiyeshea ke jagoranta ya mika rahotonsa zuwa ga Majalisar jihar. Alkalin alkalan jihar Kogi, Jastis Nasir Ajanah shi ne ya kafa wannan kwamitin. John kuma wanda shi ne shugaban kwamitin ya jagoranci mika rahoton binciken zuwa ga Kakakin majalisar jihar a ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba, 2019. Kakakin majalisar, Kolawole Matthew ne ya karbi rahaton daga hannun shugaban kwamitin a Majalisar jihar dake Lokoja. Da yake magana bayan mika rahoton shugaban kwamitin ya ce sun yi iya bakin kokarinsu na yin bincike na gaskiya. A cewar shugaban, John Baiyeshea, a shirye kwamitinsu yake domin amsa duk wata tambaya da ta shafi abinda rahoton nasu ya kunsa. Kuma ya kara da cewa rahoton ya kasu zuwa mujalladi uku. Read more: https://hausa.legit.ng/1267993-yanzu-yanzu-an-tsige-mataimakin-gwamnan-jihar-kogi-achuba.html

Legit Hausa

Ana saura wata daya gudanar da zaben jihar, an tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba. Majalisar dokokin jihar sun tsige Mista Achuba ne a Lokoja, babbar birnin jihar, ranar Juma'a 18 ga Oktoba, 2019.

Shugaban masu rinjaye a majalisar ya bayyana hakan ne ga manema labarai a zauren majalisar. Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Wani kwamitin binciken a kan zargin da ake yiwa mataimakin gwamnan Kogi Simon Achuba, wanda Barista John Baiyeshea ke jagoranta ya mika rahotonsa zuwa ga Majalisar jihar.

Alkalin alkalan jihar Kogi, Jastis Nasir Ajanah shi ne ya kafa wannan kwamitin. John kuma wanda shi ne shugaban kwamitin ya jagoranci mika rahoton binciken zuwa ga Kakakin majalisar jihar a ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba, 2019. Kakakin majalisar, Kolawole Matthew ne ya karbi rahaton daga hannun shugaban kwamitin a Majalisar jihar dake Lokoja.

Da yake magana bayan mika rahoton shugaban kwamitin ya ce sun yi iya bakin kokarinsu na yin bincike na gaskiya. A cewar shugaban, John Baiyeshea, a shirye kwamitinsu yake domin amsa duk wata tambaya da ta shafi abinda rahoton nasu ya kunsa. Kuma ya kara da cewa rahoton ya kasu zuwa mujalladi uku.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN