Yanzu-yanzu: FG za ta sanar da sabon allawus na masu yi wa kasa hidima - Minista

Legit Hausa
Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare ya bayyana cewa 'yan yi wa kasa hidima wato NYSC suna daga cikin wadanda za su amfana da sabon karin albashi mafi karanci.
Dare ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren Laraba.
Ya ce, "Sabon albashi mafi karanci: 'Yan NYSC za su amfana da sabon albashi mafi karanci cikin allawus dinsu.
"A sati mai zuwa, Shugaban NYSC zai bayar da cikakken bayani kan sabbon allawud din da 'yan yi wa kasa hidima za su rika karba bayan ya gana da Ma'aikatar Kudi da MYSD."
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post