Ku yi hakuri kwanan nan za a daina dauke wuta a Najeriya kwata kwata - Buhari

Legit Hausa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yan Najeriya tabbacin samun wutar lantarki mai dorewa kuma cikin sauki nan ba da jimawa ba.
Da yake magana a ranar bikin yanci na 59 a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba, Shugaban kasar yace gwamnatinsa ta yanke shawarar kawo sauyi a ma’aikatar wutar lantarki.
Yayinda tallafin kudin lantarki a gwamnatin Buhari ya doshi naira triliyan 1.5 cikin shekaru biyar, wutar lantarki da ake ba gidajen yan Najeriya ya kasance kasa da megawatts 5,000.
“Muna shirin sauya harkokin ma’aikatar wutar lantarki. A watan Agusta na wannan shekarar, Mun kaddamar da shirin Shugaban kasa akan wutar lantarki domin zamanantar da kasar a rukuni uku: farawa daga 5 Gigawatts zuwa 7 Gigawatts, sai 11 Gigawatts a 2023, sannan daga karshe 25 Gigawatts bayan,” inji Buhari.
A halin da ake ciki, shugaban kasar yace jagoranci nagari da bunkasar tattalin arziki ba za su tabbata ba tare da zaman lafiya, ingataccen tsaro da kuma aminci a kasa. Yace dole ne a yabawa dakarun sojin Najeriya da ke ci gaba da sadaukar da rayukansu domin kare martabar kasar nan wajen yakar kungiyar masu tayar da kayar ta Boko Haram a tsawon shekaru hudu da suka gabata.
DAGA ISYAKU.COM 

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN