'Yan kai gawa sun ranta ana kare bayan kammala binne gawa sunji tana magana daga cikin kabari


Legit Husa

A ranar 13 ga watan Oktobar nan ne wata mata mai suna Andrea Bradley ta sanya wani bidiyo a shafinta na sada zumunta na Facebok, inda aka nuno yadda ake yin zaman makokin mahaifinta.

Bradley wacce take zaune a kasar Ireland, ta bayyana cewa mahaifinta shakiyyi ne wanda a koda yaushe yake son yin abinda zai bada dariya, bidiyon dai ya bayyana yadda mahaifinta ya mutu.

Sai dai kuma a lokacin da 'yan uwa da abokan arziki suke ta faman kuka da jimamin mutuwar shi, kawai sai jin murya aka yi ta fito daga cikin akwatin gawa.

An jiyo mutumin yana cewa: "Ku bude ni na fito, akwai duhu sosai!" Ga dai abinda aka rubuta a kasan bidiyon: "Ba shi da aiki sai tsokana da zolaya, tsokanar ka tayi daidai Baba, ka sanya mu dariya a lokacin da muke bukatar ta, ina sonka har abada."
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post