Yan Hisba sun kama karuwai 93 a Kano, 23 cikinsu na dauke da cutar HIV

Legit Hausa


 Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta kama mutane 93 da ake zargin karuwai ne kuma 23 cikinsu suna dauke da kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki.
Kwamandan hukumar na jihar, Sheikh Muhammad ibn-Sina ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis.

Ya ce jami'an hukumar sun kai samame a Badume Joint a karamar hukumar Bichi a jihar inda ya yi kaurin suna a matsayin matattaran karuwai da wasu masu aikata laifi.

Sheikh Sina ya ce, "Cikin wadanda muka kama 23 mata da maza hudu, gwajin da likita ya yi ya nuna suna dauke da cuta mai karya garkuwar jiki da HIV."
Ya ce an gudanar da sumamen ne don tsaftace jihar kamar yadda ya ke cikin dokar jihar da ta hana karuwanci da sauran ayyukan masha'a.

Ya kara da cewa rundunar ta Hisbah za ta cigaba da ya ki da dukkan ayyukan da ka iya gurbata tarbiyar al'umma jihar a duk inda ake aikata shi.

A wani rahoton kuma mun kawo muku cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kafa kwamitin bincike mai dauke da mutum 16 don bin didigin yadda aka sace wasu yara 9 'yan Kano aka kai su jihar Anambra.

Rundunar 'yan sanda sun kama wasu mutane da ake zargi da hannu wurin safarar kananan yaran zuwa jihohin na Kudu.

Baya ga yara taran na farko, 'Yan sanda sun kuma sake ceto wasu kananan yaran biyu a hannun wasu masu safarar kananan yaran a jihar ta Anambra.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapphttps://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN