Yadda zaman kotu ta kasance tsakanin Gwamnatin jihar Kebbi da Aisha tare da Nasiru

Nasiru Jatau , Aisha Zakari da Jaririyarta tare da Bbangida
An fara shari'ar da fitaccen Lauya dan kare hakkin bil'adama Barista A.A Fingilla ya shigar a gaban wata babban Kotun tarayya a garin Birnin kebbi, inda yake neman Gwamnatin jihar Kebbi tare da hukumar tsaro ta Department of State Services DSS, rundunar jihar Kebbi su biya Nasiru Jatau tare da matarsa Aishaa Zakari, har da Jariyayarsu da kuma babban dansu Babangida, diyyar Naira Miliyan dari biyar sakamakon cin zarafi da Gwamnati ta sa DSS ta yi masu.

An fara shari'ar ne da karfe12:04 na ranar Juma'a 4 ga watan Oktoba, 2019. Lauyoyi hudu ne suke kare Gwamnatin jihar Kebbi, wanda suka hada da Bagudu U. Abubakar, Hudu Garba, Kubura Shu'aibu Diri, wacce ita ce mataimakiyar babban mai shigar da kara a madadin Gwamnatin jihar Kebbi, da Shamsuddeen Ja'affar daga ma'aikatar shari'a na jihar Kebbi.

A bangaren masu kara kuwa, Lauyoyin da suka tsaya wa masu kara sun hada da jagoran Lauyoyin Barista A.A. Fingilla, Bashir Umar, da Mudassir Sale.

A bangaren hukumar DSS kuwa, Barista D.I Namata ne ke kare hukumar a zaman wannan Kotu.
Wasikar da DSS ta ce Aisha ta aika wa Gwamna Atiku Bagudu. Ba sunan wanda ya aika ba na wanda aka aika masa

Bayan da Lauyan masu kara watau Barista Fingilla ya gabatar da nashi bayani ga Kotu, bisa tsarin shari'a dangane da takardun shari'a da ya gabatar wa Kotu a baya, Fingila ya tsaya kai da fata cewa akwai kuskure a takardun kariya na shari'a da wadanda ake kara suka gabatar a gaban Kotu. Daga karshe ya bukaci Kotu ta yi watsi da duk wata kariya da Lauyoyin wadanda ake kara suka gabatar. Daga karshe ya ce

" Ya mai girma mai shari'a, makasudin wannan kara shine kan cin zarafi ta hanyar kama wadanda muke wakilta kuma aka tsare su har kwana 13, Lauyoyin wadanda ake kara basu musanta haka ba".
Wannan shine wasika da aka aika  wa Nasiru Jatau domin ya halarci intervie, ga lambar wanda ya aiko da wanda aka aika masa

Amma a nashi gabatarwa a Kotu, jagoran Lauyoyin Gwamnatin jihar Kebbi, Barista Bagudu, ya gabatar da bayanan shari'a tare da bayar da misalai daga madogaran shari'a , dalilai da suka sa yake bukatatar Kotu ta yi watsi da korafe korafen Lauyan masu kara.

Bayan Alkalin Kotu Jastis Bassey Onu, ya saurari dukannin bangarorin guda biyu, ya daga shari'ar. Amma bai fadi ranar da za a ci gaba da shari'ar ba. Sai dai ya ce " Kotu ta daga wannan shari'a, kuma Kotu za ta sanar da Lauyoyin masu kara da wadanda ake kara ranar da Kotu za ta sake zama domin bayar da hukunci. Kuma duka bangarori su mika wa Magatakardan wannan Kotu, takardun madogaran shari'a da kuka ambato ta hanyar bayar da misali da su ".
 
DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN