Yadda ake gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Kebbi


Legit Hausa

An fara kada kuri'u lami lafiya a rumfar zabe ta Dakta Gukama mai lamba 007 da kuma rumfar zabe ta G/Kundi a mazabar Nasarawa da ke karamar hukumar Birnin Kebbi amma mutane kalilan ne suka fito zaben.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN), an fara zaben karamar hukumar ta Birnin Kebbi tun karfe 7 na safiya bayan da aka kawo kayayyakin zaben kuma jami'an zaben suka hallara. Jami'an Hukumar Zabe na Jihar Kebbi (KEBSIEC) sun isa rumfunan zabe misalin karfe 7 na safe yayin da aka fara jefa kuri'ar farko misalin karfe 8.43 na safe.

Daily Trust ta ruwaito cewa an fara zabe a mafi yawancin rumfunan zabe misalin karfe 9 na safe inda jami'an 'yan sanda suka hallara don tabbatar da tsaro. A mafi yawancin rumfunan zaben ana gudanar da zaben da tantance masu zabe a lokaci guda ne sai dai mutanen da suka fito ba su da yawa.

An baza jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya da na Hukumar tsaro ta NSCDC a rumfunan zaben duk da cewa al'umma ba su fito ba sosai. Jami'in zabe na rumfar zabe ta G/Kundin Zouro, Abidina Abubakar ya ce ya isa rumfar zaben karfe 7 na safe kuma suna tsamanin mutane za su fito domin su kada kuri'unsu.

 Wani jami'in zaben a rumfar zaben Dakta Guluma, Faruku Muhammad ya ce dukkan kayayyakin zaben sun iso kuma zaben na tafiya lami lafiya. Wani mai zabe, Abdulkarim Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana farin cikinsa kan yadda zaben ke tafiya lafiya kuma ya yi addu'an Allah yasa a gama lafiya.

Shima gwamnan jihar, Atiku Bagudu ya ya yi murnar ganin yadda mata suka fito kwansu da kwarkwata. Yayin kada kuri'arsa a rumfar zaben Mai Alelu a mazabar Nasarawa a Birnin Kebbi, gwamnan ya yabawa KESIEC kan kokarin da tayi na samar da isasun kayayyakin zabe. Ana gudanar da zabukan ne a kananan hukumomi 21 na jihar.
 

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN