Sojin kasar Lebanon sun fara wani muhimmin aiki bayan murabus na Frayi minsta Hariri

Jami'an tsaro sun fara kawar da shingaye da masu zanga-zanga suka sa a manyan hanyoyi bayan rundunar sojin kasar Lebanon ta bayar da bayar da umurnin cewa dole ne masu zanga-zanga su bari a ci gaba da gudanar da rayuwa cikin walwala.

Wannan umurni daga sojin kasar ya fito ne ranar Laraba kwana daya bayan Frayi Ministan kasar Lebanon Saad Hariri ya bayar da sanarwar yin murabus daga mukaminsa, wanda ya zo yan awowi kafin shugaba Michel Aoun  ya gabatar da jawabi ga al.umman kasar.

Shugaba Aoun dai bai yarda da murabusa na Frayi Minista Hariri ba , lamari da ya haifar da damuwa da tashin hankalin siyasa tare da bayar da gargadi daga kasashe da ke makwabta da kasar ta Lebanon .
Hariri ya yi murabus ne ranar da zanga-zangan talakawan kasar ya cika rana ta 13, inda suke bukatar manyan yan siyasaar kasar su yi kaurace wa fagen siyasa, sakamakon rashin ingantaccen ababen more rayuwa ga talakawan kasar, tabarbarewar arzikin kasa, cin hanci da rashawa da kuma al'mubazzaranci da dukiyar kasa.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post