Legit Hausa
Justis Obiora A. Egwuatu na babbar kotun Kano ya sanya ranar
Laraba 23 ga watan Oktoba a matsayin ranar da kotun zata yanke hukunci bisa
karar cin-zarafi da Amina Mohammed Amal ta shigar a kan cewa Hadiza Aliyu Gaon
ta yi mata.
A ranar Laraban ne kotun za ta dubi wannan karar domin
sauraron hujjoji daga bangaren Hadiza Gabon wadda ita ce ake kara. Haka kuma
ana sa rana a ranar za a yita ta kare game da karar gaba dayanta.
Amal a cikin karar da ta shigar ta nemi kotu ta ba Gabon
umarnin ba ta hakuri a gaban jama’a sannan kuma ta biyata tarar miliyan N50 saboda
raunin da ta jimata a fuska. Sai dai kuma bangaren lauyoyin Gabon sam ba su
aminta da wannan abubuwa da Amal ta bukata ba, inda suka cewa ai abin gaba
dayansu ya faru ne a can wani wuri na daban inda bai cikin hurumin kotu.
Da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis 3 ga watan
Oktoba jim kadan bayan fitowa daga farfajiyar kotun, jagoran lauyoyin Gabon,
Barrister Sadiq Sabo Turawa ya ce: “Mun riga da mun mika duk wani bayani da
kotun ke bukata na a dakatar da abinda Amal din ta nema.”
A dayen bangaren kuwa, lauyan Amal, Barrister Faruk Umar ya
musanta bayanan takwaransa inda ya ce: “Muna jiran ranar cigaba da shari’a ne
saboda mun san cewa hujjojinmu masu nagarta ne kwarai da gaske.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN