Nan da makonni 6, sabbin jiragen kasa 20 zasu shigo Najeriya daga Sin - Amaechi


Legit Hausa

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa sabbin jiragen kasa 20 za su shigo Najeriya domin safarar jama'a a filin jirgin kasa Abuja/Kaduna da Lagos/Ibadan nan da makonni shida masu zuwa. Amaechi ya bayyana hakan ne a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwa Abuja yayinda ya dawo daga kasar Sin.

Ya yi hira da manema labarai kan tafiyar da yayi zuwa Sin da kuma abubuwan da ya je yi. Yace: "Abubuwa biyu suka kai mu, mafi muhimmanci domin mu sayi sabbin jirage. Duk suna kasa. Za'a yi makonni shida kafin sun iso Najeriya kuma za'a yi mako daya kafin tantancesu a tashar ruwa."

"Amma ga jiragen Legas, zai fi sauki, cikin kwana daya ko biyu kadai za'a fara amfani da su. Amma jiragen Abuja sai an kwashe mako daya kafin su iso nan." "Muna kyautata zaton samun sabbin jirage 20, 10 na Abuja-Kaduna, 10 na Legas -Ibadan a matsayin somintabi kawai, za'a karo wasu kuma idan muka kammala layin dogon Legas-Ibadan."

Ministan ya bayyana cewa yayinda ganin sabbin jiragen a Sin, ya gwadasu da kansa. Ya ce wadannan sabbin sun fi wadanda ake amfani da su yanzu kyau a zamanance. He added that more trains were still being built for Nigeria and the next batch would be delivered as soon as they are ready. Ya kara da cewa akwai sabbin jiragen da ake kerawa Najeriya musamman kuma ana kammala kerawan za'a turosu.
 

DAGA ISYAKU.COM

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post