Mutuwan mai laifi a hannun yansanda: Shugaban yansanda na fuskantar tuhuma

Daga Leadershipayau.com


A ranar Talata ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jos a jihar Filato, ta umurci babban Sufeton rundunar ‘yan sanda da dan sanda Abba Kyari, mai mukamin mataimakin Kwamishina, wanda kuma ke jagorantar wata runduna ta musamman mai lakabin IRT da su gabatar da wani mai laifi a gabanta, da rai ko a mace.   

Alkaliyar kotun, Jastis Dorcas Agishi, ta bayar da wannan umurnin ne bayan D. G. Dashe, Lauyan mutumin da aka kama mai suna Mista Nanpon Sambo ya shigar da korafi a gabanta, inda ya yi zargin cewa mutumin da yake kare wa ya mutu a hannun rundunar ‘yan sanda a Abuja. 

Alkaliyar kotun ta bawa manyan jami’an ‘yan sandan sati biyu domin su fito da mai laifin ko kuma su fuskanci fushin doka. Dashe ya fara rubuta takardar koke zuwa kotun a ranar 25 ga watan Satumba domin neman a tilasta IGP da Kyari su gabatar da Sambo a gaban kotu bayan kama shi da rundunar ‘yan sanda ta yi bisa zarginsa da mallakar bindigu ba bisa ka’ida ba. 

“Idan ma rundunar ‘yan sanda ta bizne mai laifin bayan ya mutu, ina umurtar ta hako shi daga kabari tare da kai gawarsa asibitin koyar wa na Jami’ar Jos domin gudanar da binciken masana a kansa,” A cewar ta. Agishi ta yi gargadin cewa za ta dauki mataki mai tsanani matukar sati biyu suka cika ba tare da IGP da Kyari sun yi biyayya ga umurnin da ta bayar ba.

Alkaliyar kotun, Jastis Dorcas Agishi, ta bayar da wannan umurnin ne bayan D. G. Dashe, Lauyan mutumin da aka kama mai suna Mista Nanpon Sambo ya shigar da korafi a gabanta, inda ya yi zargin cewa mutumin da yake kare wa ya mutu a hannun rundunar ‘yan sanda a Abuja. Alkaliyar kotun ta bawa manyan jami’an ‘yan sandan sati biyu domin su fito da mai laifin ko kuma su fuskanci fushin doka. 

Da ya fara rubuta takardar koke zuwa kotun a ranar 25 ga watan Satumba domin neman a tilasta IGP da Kyari su gabatar da Sambo a gaban kotu bayan kama shi da rundunar ‘yan sanda ta yi bisa zarginsa da mallakar bindigu ba bisa ka’ida ba. 

“Idan ma rundunar ‘yan sanda ta bizne mai laifin bayan ya mutu, ina umurtar ta hako shi daga kabari tare da kai gawarsa asibitin koyar wa na Jami’ar Jos domin gudanar da binciken masana a kansa,” A cewar ta. Agishi ta yi gargadin cewa za ta dauki mataki mai tsanani matukar sati biyu suka cika ba tare da IGP da Kyari sun yi biyayya ga umurnin da ta bayar ba.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari