Jaruma Rahama Sadau ta sake barota a masana'antar Kannywood, karanta abunda ta yi

Legit Hausa
Jaruma Rahama Sadau tayi kaurin suna a masana'antar Kannywood wajen sanya maudu'in da za ayi ta kace-nace a kai, zamu iya cewa tun farkon bayyanar ta ya zuwa yanzu jarumar ba ta shafe watanni uku ba tare da tayi wani abu da zai jawo magana a kafafen sadarwa ba.
Koda yake wasu na ganin da gangan 'yan fim da mashahuran mutane kanyi abubuwa na jan magana don kar a mance da su, domin wasu sunyi ittifaki da zarar an daina jin duriyar ka tofa kasuwar ka ta mutu kenan don haka sun gwammace ayi ta batun su koda na Allah wadai ne dan dai sunansu da fuskokinsu su cigaba da karakaina a kafafen sadarwa da mujallu.
A yau wannan jaruma dai wani hoto ta wallafa a shafin ta inda aka ganta tana sumbatar wata mace 'yar uwarta inda wallafa hotunan keda wuya akayi caa a kanta da korafi inda har wasu shafuka suka fara wallafa hoton suna fashin baki a kai.
Koda yake mu baza mu kalli wannan ta fuskar da akasarin mutane ke kallon abun ba in muka yi la'akari da cewa a 'yan kwanakin nan mafi yawancin hotunan jarumar da mata 'yan uwanta tana kusantar su sosai fiye da kima wanda zamu iya danganta hakan da karatu da tayi a kasar waje wanda hakan ba komai bane a gurin turawa masu jajayen kunnuwa, amma a nan gida hakan ya zama abin magana.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari