Hukumar DSS ta yi magana bayan sakin kasurgumin dan damfara a Kano

Legit Hausa Hukumar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) reshen jihar Kano, ta musanta zarginsu da ake yi da sakin Yunusa Ado da ake z...

Legit Hausa
Hukumar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) reshen jihar Kano, ta musanta zarginsu da ake yi da sakin Yunusa Ado da ake zargi da damfarar jama'ar naira miliyan 18.
A makon da ya gabata ne hukumar jami'an tsaron ta farin kaya ta kama Yunusa bayan samun bayanan sirri a kan al'amuransa. Hukumar ta mikashi ga babbar kotun majistare da lamba 72 Normansland inda aka aje shi a gidan maza.
Babban jami'in hukumar wanda ya zanta da jaridar Solacebase a Kano kuma ya bukaci a boye sunansa, ya ce, "A matsayin mu na jami'ai, muna aikinmu na cafke wadanda ake zargi da damfara kuma mu mikasu ga kotu, wanda hakkin alkali ne ya sake su ko yasa a ajiye su a gidan yari ko kuma ya bayar da belinsu".
"Amma kuma abin mamaki, sai aka ga Yunusa na yawo hankali kwance a daren da muka kama shi, hakan na nuna cewa alkalin kotun da aka gurfanar da shi ne ya bada belinsa", in ji jami'in.
Ana zargin Yunusa Ado ne da sanya yaransa yi wa jama'a rijista da sunan zai sama musu gurbi a shirin N-Poverty, inda suke karbar N30,000 zuwa N50,000 daga kowanne mutum. An gano cewa ya yi wa mutane sama da 5,000 irin wannan rijistar bogin.
Bayan samun makuden kudade daga damfarar da ya yi, Yunusa Ado ya siyawa mahaifiyarsa gida na naira miliyan shida a cikin Kano.
Wata majiyar a cikin jami'an farin kayan ta ce, Yunusa ya amsa laifukansa a gaban kotu inda ya roki yafiya tare da alkawarin zai maidawa wadanda ya damfara kudadensu.
Kamar yadda majiyar ta sanar, " Daga nan ne alkali ya bukaci a ajiyeshi a gidan maza tare da dage shari'ar zuwa Talata mai zuwa. Amma abin mamaki sai aka ganshi yana yawo a gari. Bazamu iya tambayar alkalin ba, amma babu hannunmu a ciki."
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
IDAN KA GAN WANI ABU NA FARUWA, HANZARTAB KA SANAR DA MU A ISYAKULABARI@GMAIL.COM
Name

'YANSANDA,1,AL-AJABI,22,AREWA,45,BIDIYO,147,BINCIKE,1,BIRNIN-KEBBI,375,BOLLYWOOD,2,BUHARI,10,DUNIYA,110,ENGLISH,27,FADAKARWA,126,FASAHA,14,FITACCEN LABARI,19,HOTO,175,HOTUNA,90,JAKAR MAGORI,1,LABARI,2982,NISHADI,283,OSCAR,2,Samaila Yombe,42,SANARWA,31,SHARHI,16,SIYASA,387,TARIHI,11,TSARO,354,WASANNI,18,
ltr
item
ISYAKU.COM: Hukumar DSS ta yi magana bayan sakin kasurgumin dan damfara a Kano
Hukumar DSS ta yi magana bayan sakin kasurgumin dan damfara a Kano
https://1.bp.blogspot.com/-9xvCNw6YH2Q/XaNYK0MUvQI/AAAAAAAAXaM/mUkvfXZmLsA4MIqlgQE95xFZYgcExBBLgCLcBGAsYHQ/s320/images-87.jpeg
https://1.bp.blogspot.com/-9xvCNw6YH2Q/XaNYK0MUvQI/AAAAAAAAXaM/mUkvfXZmLsA4MIqlgQE95xFZYgcExBBLgCLcBGAsYHQ/s72-c/images-87.jpeg
ISYAKU.COM
https://www.isyaku.com/2019/10/hukumar-dss-ta-yi-magana-bayan-sakin.html
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/2019/10/hukumar-dss-ta-yi-magana-bayan-sakin.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy