Har yanzu ba a kama Zakin da ya tsere daga gidan adana namun daji a Kano ba


Legit Hausa

Sabanin rahotanni daga wasu kafofin watsa labarai na kasar nan suka yada dangane da cewa an samu nasarar cafke zakin da ya tsere daga gidan adana namun daji na jihar Kano, mahukuntan gidan sun yi karin haske. Mahukanta a gidan adana namun dajin Kano sun ce ya zuwa yanzu ba a kai ga kama zakin da ya kufce ba daga wurin da aka killace shi.

Da yake ganawa da manema labarai na jaridar Kano Focus dangane da tserewar zakin, shugaban gidan adana namun dajin, Alhaji Saidu Gwadabe, ya ce tuni aka baza kwararru a fannin kama zakuna domin lalubo inda ya buya tare da mayar da shi wurin killatarsa.

A cewar Gwadabe, ko kadan batun da wasu kafofin watsa labarai suka yada dangane da kama zakin ba gaskiya bane, domin kuwa ya zuwa yanzu harbin da aka yi wa Zakin har sau biyu da harsashi mai sanya bacci bai yi tasiri ba inda ko gizau bai yi ba, sai dai ya nemi al’umma da su kwantar da hankulansu.

 Dangane da irin ta'asar da Zakin ya tafka bayan kufcewarsa, ya yi wa akuyoyi jina-jina biyon bayan afkawa garkensu da ya yi wanda harabar ma'adanar namun dajin.

Sai kuma jimina guda a wadda har yanzu an turke shi a kejinta. Ko a shekarun baya dai gidan adana namun dajin na jihar Kano ya fuskanci tserewar Kadaji wanda lamarin makamancin wannan ya haddasa tsoro a zukatan al'umma musamman wadanda ke makotaka da gidan adana namun dawan.
 


DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN