Gwamnoni 9 sun hallarci daurin auren 'yar Matawalle

Legit Hausa
Gwamnoni tara da tsaffin gwamnoni da dama suna daga cikin wadanda suka hallarci daurin auren 'yar gwamnan jihar Zamfara, Ruqayya Matawalle a ranar Asabar a garin Maradun.
Gwamonin sun hada da gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal; gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya; gwamnan Imo, Chukwuemeka Ihedioha; gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow da gwamnan Borno, Babagana Zulum.
Tsaffin gwamnonin da suka hallarci daurin auren sun hada da Rabiu Musa Kwankwaso, Sule Lamido da Ahmad Sani.
Gwamna Tambuwal shine waliyin amaryar Ruqayya inda ya bayar da ita ga wakilin angon, Madakin Katagum, Alhaji Abdullahi Babani a auren da aka dayura a fadar sarkin Maradun.
An daura auren kan sadaki naira N100,000 da aka biya lakadan.
Gideon Sammani, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin siyasa ne ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari a wurin daurin auren.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa 'yan majalisar tarayya da na jihar da manyan 'yan siyasa da sarakuna da masu rike sa sarautun gargajiya daga sassa daban-daban na kasar sun hallarci daurin auren.
DAGA ISYAKU.COM 

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari