Da sauran rina a kaba, Zakin da ya kwace a Kano ya sake cin Jimina daya da awaki 2 (Bidiyo)


Legit Hausa

Ma'aikatan gidan Zoo na jihar Kano sun bayyana cewa idan hanyoyin da ake bi na damke Zakin da ya kwace ranar Asabar ya gagara, za'a harbe dabban domin kare rayukan jama'a.

Daily Nigerian ta ruwaito. Mun kawo muku rahoton cewa Zakin ya fasa cikin gidan Jimina kuma ya lashe daya kafin jami'an gidan suka turashi cikin kejin akuyoyi kuma hallaka biyu.

Diraktan gidan Zoo na Kano, Saidu Gwadabe, ya bayyanawa manema labarai a daren Lahadi cewa har yanzu ana cigaba da kokarin cewa na kama Zakin da ransa. Gwadade yace kawo yanzu, Zakin ya kashe Jimina biyu da akuyoyi da dama: "Zakin ya kwace gidan Jiminan kuma ya cinye biyu," a cewarsa.

Ya kara da cewa a gayyato masana kiwon dabbobin gidan Zoo na kasa sun dira Abuja domin bada gudunmuwarsa wajen kama dabban da ya kwace. Ya ce har harbeshi da alluran kashe karfin jiki 10ml bayan ya shanye 1.5m kuma ba tayi masa tasiri ba.

KALLI BIDIYO:

 
 
DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post