Cikakkun labaran dare Laraba 30, Oktoba 2019

LABARAI Shugaban ‘Yan Sanda Na Fuskantar Tuhuma Kan Mutuwar Mai Laifi A Hannunsu Published 22 mins ago on October 30, 2019 By Ammar Muhammad A ranar Talata ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jos a jihar Filato, ta umurci babban Sufeton rundunar ‘yan sanda da dan sanda Abba Kyari, mai mukamin mataimakin Kwamishina, wanda kuma ke jagorantar wata runduna ta musamman mai lakabin IRT da su gabatar da wani mai laifi a gabanta, da rai ko a mace. Alkaliyar kotun, Jastis Dorcas Agishi, ta bayar da wannan umurnin ne bayan D. G. Dashe, Lauyan mutumin da aka kama mai suna Mista Nanpon Sambo ya shigar da korafi a gabanta, inda ya yi zargin cewa mutumin da yake kare wa ya mutu a hannun rundunar ‘yan sanda a Abuja. Alkaliyar kotun ta bawa manyan jami’an ‘yan sandan sati biyu domin su fito da mai laifin ko kuma su fuskanci fushin doka. Dashe ya fara rubuta takardar koke zuwa kotun a ranar 25 ga watan Satumba domin neman a tilasta IGP da Kyari su gabatar da Sambo a gaban kotu bayan kama shi da rundunar ‘yan sanda ta yi bisa zarginsa da mallakar bindigu ba bisa ka’ida ba. “Idan ma rundunar ‘yan sanda ta bizne mai laifin bayan ya mutu, ina umurtar ta hako shi daga kabari tare da kai gawarsa asibitin koyar wa na Jami’ar Jos domin gudanar da binciken masana a kansa,” A cewar ta. Agishi ta yi gargadin cewa za ta dauki mataki mai tsanani matukar sati biyu suka cika ba tare da IGP da Kyari sun yi biyayya ga umurnin da ta bayar ba.

Read More at: https://hausa.leadership.ng/2019/10/30/shugaban-yan-sanda-na-fuskantar-tuhuma-kan-mutuwar-mai-laifi-a-hannunsu/

RFI HAUSA

Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar adawa PDP Atiku Abubakar ya shigar a gabanta, inda yake kalubalantar nasarar da Muhammadu Buhari na APC ya samu a zaben shugabancin kasar na watan afrilun 2019.
Shugaban Kotun, mai shari’a Tanko Muhammad, ya ce bayan share tsawon makonni biyu suna bincikar takardun da ke kunshe da korafe-korafen da jam’iyyar PDP ta gabatar a game da yadda zaben ya gudana, daga bisani sun gano cewa ba wata hujjar da jam’iyyar ta gabatar.
Saboda haka ne a cewar shugaban kotun aka yi watsi da wannan kara, bayan da illahirin alkalai bakwai suka amince da matakin.

Wannan hukunci na kotun koli ya kawo karshen shari’ar da ta hada Atiku Abubakar dan takarar PDP da Muhammadu Buhari na APC, bayan share tsawon watanni 8 a gaban kotuna daban daban na kasar.
A lokacin da aka gudanar da zaben cikin watan fabarairun da ya gabata, Muhammadu Buhari na APC ya samu 56% na kuri’un da aka kada, yayin da Atiku Abubakar na PDP ya samu 41%.

BBC HAUSA

Har kawo yanzu ba a iya tantance kowace irin cuta ce ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 18 a kauyuka uku na karamar hukumar Matazu da ke jihar Katsina ba.
Jami'i mai kula da shirin lafiya a matakin farko na karamar hukumar, Abdulsalam Umar Jikamshi ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu dai mutum 45 ne suka kamu da cutar, inda 18 kuma suka mutu.
Abdussalam Jikamshi ya kara da cewa "wadanda da suka kamu da cutar sun yi fama da zazzabi da ciwon kai da amai."

Ya kuma kara da cewa tuni gwamnatin jiha ta aike da samfirin cutar zuwa birnin Legas domin yin gwaji wajen gano cutar da ke kisan mutanen
Duk da cewa har yanzu ba a fahimci cutar da ke mamaya a karamar hukumar ba, Abdussalam Jikamshi ya ce ibtila'in ba zai rasa nasaba da rashin ruwan sha mai kyau da rashin kyawun muhalli da yankunan ke fama da su.

To sai dai wasu rahotanni na cewa adadin mutanen da suka mutu ya fi 18.
Amma Shugaban karamar hukumar ta Matazu, Kabir Faruk Matazu ya shaida wa BBC cewa "rahotannin da muke samu daga kauyuka abin babu dadi. Ba za mu iya tantance hakikanin mutanen da suka mutu ko kamu da cutar ba."

"Kasancewar wasu ba sa zuwa asibiti sannan wasu na tafiya wurin masu maganin gargajiya ya sa muke la'akari da kididdigar mutanen da suka zo asibiti."
Daga karshe shugaban karamar hukumar ya ce gwamnatin jiha na iya bakin kokarinta wajen ganin ta dakile cutar daga bazuwa.

VOA HAUSA

An ce karen bana maganin zomon bana. A yayin da 'yan damfara ta yanar intanet ke bullo da wau sabbin salo, haka su ma kungiyoyi da hukumomin da ke yaki da su ke bullo da sabbin matakan kama su.
Yawan damfarar mutane ta hanyar yanar intanet na karuwa a Najeriya, inda mutane kan yi asarar kudi da kuma ta kai ma a na biyan kudin fansa ta hanyar damfarar da ke da wuyar ganewa mai suna “BIT-COIN

Ibrahim Kyauka da Jamilu Muhammad na kungiyar yaki da ‘yan damfarar ta Najeriya sun bukaci jama’a su bullo da hanyar rufe layin wayar su da lambobin sirri don hakan ya hana samun bayanansu na boye in an sace masu waya ko kuwa in wayar ta bata.

Hakanan sun bukaci mutane su kauce wa amfani da ranar haihuwar su a matsayin lambar sirri ta katin daukar kudinsu na banki wato ATM.

Shin yaya hanyar hada-hadar kudi ta BIT-COIN ta ke aiki?.

Jamilu Muhammad ya ce rashin kwarewa ya sa a ka kama wani matashi da ya sace wata yarinya a Abuja da amsar diyya ta BIN-COIN.

Kazalika sun bukaci jama’a su guje wa bayyana asiran tafiye-tafiyensu ta kafofin sada zumunta don kauce wa sharrin miyagun iri.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post