Buhari ya sauka Makka domin gudanar da Umrah, duba abin da ya faru (Bidiyo)


Legit Hausa

Da yammacin Alhamis, Shugaba Muhammadu Buhari ya isa birnin Makkah, domin gabatar da ibadar Umrah bayan kammala halartan taron sanya hannu jari na tsawon kwana uku a birnin Riyadh. Shugaba Buhari ya dira filin jirgin saman Sarki AbdulAziz ne misalin karfe 7:05 na Magariba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta bada rahoton cewa shugaba Buhari ya samu kyayyakwar tarba daga wajen mataimakin gwamnan garin Makkah, Bader bin Sultan bin AbdulAziz da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar a filin jirgin saman Sarki AbdulAziz.

Tuni shugaba Buhari da wadanda suka rakashi sun sanya izari da rida'i. Daga cikin wadanda zasu gudanar da Umrah tare da shi sune gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari; gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu da sauransu.

Kalli bidiyon:


DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN